Spread the love
Hajiya Fatima Inno Attahiru

Muhammad M. Nasir.

Hajiya Fatima Inno Attahiru sananan ‘yar siyasa ce dalibar ilmi a Sakkwato, dake fafutika a kungiyoyin addinin musulunci daban-daban a Nijeriya  domin tabbatar da hakkin mata da adddini da al’ada suka aminta da shi, ba ta damu da batancin da wasu ke yi ba na cewa su wakillan yahudawa ne, a zantawarta da Managarciya ta yi Magana kan shekarar farko ta gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal in da take ganin an samu nasara a tafiyar.

“Gwamnatin Tambuwal yanda take gudanar da abubuwanta tana tafiya yanda yakamata nasara ce maras kwakwazo(silence achiever) ana aiki sosai sai dai ba za’a iya gamsar da kowa ba, alkawalin da ya dauka a farkon wa’adinsa ba zai iya cika shi gaba daya ba, saboda yanda ya samu gwamnatin, amma kowa yasan yana kokari a wajen walwalar jama’a, kuma ya shirya gudanar da manyan aiyukka dafatan zai kammala su kafin wa’adin mulkinsa ya kare.”  A cewar Hajiya Fatima Inno.

An bayyana jihar Sakkwato a matsayin wadda tafi talauci a Nijeriya mi za ki ce a bayanin? “Gaskiya na ji bakin ciki da wannan bayanin sai dai ba a yau aka fara ba, amma abin da nake son mutane su fahimta dalilin da ya sa muke da talauci ba laifin gwamnati kadai ba ne, akwai ‘yan kasuwarmu da ba su iya hada kai su samar da wata masana’anta da mutanenmu za su yi dogaro da ita, babu aminci a tsakaninsu, matasanmu ba su san ciwon kansu ba, ko an fito da shirin koyon sana’a ba su yi, masu kudinmu ba su taimako duk kokarin da gwamnati ke yi ba mu taimaka mata, an bar komi sai ita, bayan akwai abin da za ka yi wa jama’a ba sai an jira gwamnati ba.” In ji Hajiya.

Da ta juya kan fafutikar da take yi na mata su shigo a dama da su a harkokin rayuwa ta ce gwamnan Sakkwato yasan mata sun taka rawar gani a zabensa kuma ya yi masu gwargwado, sai dai akwai bukatar wuce abin da aka yi masu a jihar nan, yakamata a samu mata kwamishinoni kamar guda 7, mace uku sun yi kadan a majalisar zartarwa jiha da sauran wurare yakamata gwamna ya duba domin mata ba wani abin tunaninsu sama da al’umma sabanin maza.     

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *