Spread the love

Mahara sun kashe mutum 70 a karamar hukumar Sabon Birni kwana daya bayan Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar ta’aziyar mutane 14 da maharan suka kashe ta hanyar yiwa wasu yankan rago a kauyen Gajit ciki har da mai garinsu dake yankin a ranar Sallah.


Abu kamar ya wuce za a dauki mataki sai a jiya Laraba maharan sun yiwa wasu kauyukka biyar kawanya da nisansu bai wuce kilomita biyar da hidikwatar karamar hukumar Sabon Birni ba. 


Maharan dauke da muggan makamai saman babura sun fi 40 sun shigo kauyukkan ne da misalin karfe ukun rana(3pm) a Laraba ba sun tambayi komai ba harbin mutane kawai suka rika yi kan mai uwa da wabi haka suka rika yi tsawon lokaci a kauyukkan domin duk a wuri daya suke. Kamar yadda wata majiya a Sabon Birni ta shedawa Aminiya a waya.


Majiyar ta ce a lokacin da nake magana da  ke kusan duk mutanen dake kauyukkan Sabon Birni sun tashi don gudun wani hari, domin maharan sun sauya salon hari a baya in sun zo dabbobinmu da kudade ne za su tafi da su yanzu rayuwarmu suke nema.


“Bayan maharan sun wuce da dare mutane suka shiga neman ‘yan uwansu zuwa yanzu an gawar mutane 70 a Garki 26, Dan Aduwa 13, Masawa 20, Karine 8,Kazari 3, wasu sun shiga daji nema ‘yan uwansu zuwa yanzu ba su dawo ba, wadan da suka yi rauni ba a ma maganarsu suna da yawa sosai akwai wadan da aka harba a bangarorin jiki da wadan da suka karye a kafa da samun rauni a jiki wajen tserar da rayuwarsu. A saman hanyarsu ta zuwa kauyukkan sun yi ta harbe mutane duk wanda ya hada ido da su sai sun kashe shi” a cewarta.


Majiyar ta zargi jami’an tsaron yankin da sakaci a matakin da ake dauka na yakar maharan a yankin, ganin duk sanda maharan suka zo wani kauye ko da za ka lalubo jami’an ba su nan bayan an kammala hari sai su zo da wani uzuri daban.


Mutanen yankin sun fara gudun hijira a wasu wurare suna barin wajen nasu domin tsirar da rayuwarsu a wannan lokacin maganar rayuwa ake yi ba dukiya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *