Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da mataimakin sa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna sun karbi gudunmawar N20Million daga bankin FCMB don ya ki da Corona.

Sanarwar haka ta fito ne daga bakin mai taimakawa gwamna akan kafafen yada labarai Salihu Tanko Yakasai, inda ya ce tallafin ya zo lokacin da ake bukata domin taimakawa Gwamnatin Jiha wajen kokarin da take yi na ganin ta shawo kan annobar Cutar Corona wato Covid-19.

Da kuma kokarin da Gwamnatin take yi na bada tallafi ga masu karamin karfi na kayan abinci domin sauwake musu halin da suke ciki musamman rashin fita aiki domin dokar hana zirga zirga a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *