Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da raba kayan tallafi a karo na biyu inda zaa rabawa mutane 50,000 a masarautar Bichi wadda ke da kananan hukumomi guda 6, wadanda hakiman su suka wakilce su kuma suke da alhakin rabawa mutanen kamar yadda aka tsara.

Kayan wanda wasu daga ciki na gwamnatin taraiya ne da kuma wadanda gwamnatin Jiha ta tara sun hada da shinkafa, masara Gero dawa da man girki. Sannan Gwamnatin jiha ta kara da kudi N2,000 ga kowanne magidancin da zaa bawa kudin cefane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *