Spread the love

Ai yanzu tun daga yadda ake gudanar da harkokin bikin auren Bahaushe a yau ake rugurguje komai da la’u’bali da al’adun asali na Bahaushe wanda koda da zamani da sauyin yanayi kada a zurme a yi abin da dana sani ka iya biyo baya wanda yanzu gashi muna ganin irin sakamakon hakan saboda yadda tarbiyya ke rushewa tsakanin ma’aurata dasu kansu ‘ya’yan da ake haifa.

Baya ga yadda ake bajakolin tsiraici da tikar raye-raye abun ba’a magana domin duk wasu al’adu kyawawa anyi watsi dasu a tufafi da ita kanta magana da kunya da yanzu ba kowa ke da ita ba a tsakanin Hausawa saboda aro bakin tadodi zuwa bakukuwan Hausawa a yau wanda ga irin illolin da suka haddasa nan na yiwa kowa ciwo a ransa.

Biki yanzu a gida ya zama kauyanci da rashin wayewa idan ba’aje ‘Event Centres’ ba ko wasu gurare daban wanda madudan kudade ake kashewa da gaske baya ga mai da guraren tamkar dandalin bajakolin tsiraici da nuna tsan-tsar kyau da daukar wankan kece raini da abubuwa marasa dadi wanda idan baka saba zuwa guraren ba sai kaji duk babu dadi da sakewa.

Raye-raye tsakanin miji da mata da tsakanin uwar amarya da ango abin ba’a magana wanda har da kida zalla domin babar amarya da ango saboda sabuwar wayewa data yiwa Hausawa yawa wanda a zamanin baya ba haka abin yake ba kunya ce da martaba juna amma yanzu abin ya lalace ya shiga rudu tsakanin Hausawa biyo bayan cusawa kansu bakin dabi’u marasa amfani acikin bukukuwansu su kuma ba’a koda aron daurin dankwalinsu balle amfani dashi.

Irin yadda ake gamutsuwa idan lamarin na manya ne ba’a magana wanda tun daga nan duk wata albarka acikin auren ake girjeta da watsi da ita.

Babu shakka muna cikin yanayi mai wuyar sha’ani idan muka kalli yadda ake shagulgulan bikin auren Bahaushe a zamanin da kuma yanzu.Babu tantama da yadda zamani ke garawa amma damu tarkato al’adu marasa amfani yana kara nauyaya matsalolin cikin aure anyi duk warkajamin da za’ayi amma yau aure gobe saki saboda sakin albarkar da akayi tundaga bikin auren kafin zuwa gida.

Wani kan iya fakewa da zamani ya canza saboda haka dole abubuwa su canza su ma shin shi daga Bahaushe abubuwa na wa aka koya daga cikin tadodinsa zuwa kabilun cikin bukukwansu?

Idan kuwa babu kaga anyi badi babu rai kenan har gara ya kwaskware tadodinsa ya ci gaba da amfani da kayansa tunda kyawawa ne masu amfani da asali.

Akwai takaici irin yadda jagula-jagular tayi yawa ta aro bakin tadodin zuwa cikin bukuwan Bahaushe.

Ko yaushe za’a lura a gyara?

Duk wasu muggan bakin al’adu da suka tsira wadanda babu su sun samo asali ne ta dalilin wacca rasa kunya da daukar aure ba kima tsakanin ma’autata a yau wanda dawo zane waccan martaba abu ne mawuyaci mutuka da gaske.Ta yadda zakaga macen aure bata dauki auren da kima ba sosai ganin yadda ake shirya auren kansa musamman tsakanin Hausawa.

Dan kida da rawa anayi domin nuna shagali da murnar da farin ciki irinsu kidan kwarya da sauran yan mata suyi rawa babu nuna tsiraici da shaidanci amma ba irin na yau ba da babu kunya ko tsaro.

Shin shi Bahaushe baya takama da tinkaho da al’adunsa ne?

Duk wanda ya rasa ka’ida to kuwa ya rasa fa’ida laaaa-shakka kamar yadda yanzu mun rasa duka biyun babj fa’idar babu kuma ka’idar baki daya bilhasalima mun zama ‘yan kwaikwayo yanzu mu kuma ba’ a kwaikwayon mu.

Zan dora insha Allah nan gaba.

Mustapha Abubakar Bichi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *