Spread the love


Daga Ibrahim Hamisu Kano.

Fitaccen jarumi a finafinan Hausa da ake kira Kannywood wanda ake cewa SARKI wato Ali Nuhu Muhammad ya ce shi ba fadakarwa ya ke ba, kuma bai taba cewa ya na fadakarwa ba. Jarimin ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan Radio Express Kano.

“Tambaya: Wace shawara za ka bayar don bunkasa wannan harka ta Fim?”

Ali Nuhu: Abu na farko shi ne duk wanda yake ganin yana da hanya da zai iya nemo hannun jari don bunkasa kasuwancin finafinan to ya yi, domin kasuwancin Fim din, shi ya fi akan yawan yin fim, in ka yi fim din ina za ka kai?.

Kuma wani lokaci za ka ji mutane suna cewa; fadakarwa mu ke yi, abin da na ke so mutane su gane shi ne  mai yin Fim ba malami ba ne mai koya maka tarbiya, a’a shi nishadantarwa ya ke ba malami ba ne mai koya tarbiya, mutum ne wanda ya ke nishadartar da kai, amma a cikin wannan nishadantar da kai da yake, kana iya samun sakonni na wasu abubuwa na gyran halayya, amma fa ba malami ba ne, za ka ji ana cewa kuna cewa kuna fadakarwa; ni na bude baki na ce maka ina fadakarwa? Ni dai aikina shi ne nishadi, yanzu kamar Fim din ‘Kanwar Duba-rudu’ ai ka ga nishadi ne. Saboda haka ya kamata mutane su gane bambancin,  nishadartarwa ne amma ana samun sakonni muhimmai wadanda suke gyara tarbiya da kuma halaye.


“Tambaya: a dukkanin finafinan da ka yi Wane fim ka fi so kuma masu kallo ma ya fi karbuwa a wajensu?”


Ali Nuhu: Fim guda biyu ne Wato Mariya da Kar ki manta da ni.
Tambaya: Shekararka nawa kana yin  Fim?


Ali Nuhu: Shekara ta 21 ina Fim.


Tambaya: Mene ne ainihin shafukanka na sada zumunta da kake amfani da shi, domin da yawa akwai na bogi?


Ali Nuhu: To ina amfani da kafafen sadarwa guda hudu:Tweeter: AlinuhuInstagram: RealalinuhuYouTube: Ali Nuhu channelFacebook: Ali Nuhu Muhammad.

“Tambaya :Mun gode da ka amsa tambayarmu Sarki Ali Nuhu”
Ali Nuhu:  ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *