Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

A wata hirar da gidan Rediyo Express dake Kano ya yi da babban jarumi sananne a masana’antar shirya finafinnai ta Kannywood Ali Nuhu ya nuna dacewar mutum ne ga taka rawa ke sanya a sanya shi fim ba wai ganin dama ce ba, ko shi ne a kamfaninsa in an shirya fim bai dace da rawar da ake son a taka ba zai shiga ba.

Kuma shi yana kokarin ya zaburar da matasa a harkar su zama jarummai duk a cikin daraktoci a masana’antar ya fi su wannan hobbasar kamar yadda ya fadi a hirar.

“…….Tambaya: Daga karshen karshen 2019 har zuwa yanzu akwai wasu Fina-finai da kai ka ke ba da Umurni za’a ga cewa akwai wasu kebantattun jarumai da kake sanyawa a Finafinanka irinsu Umar M. Sharif da Maryam Yahya da Hassana Muh’d da   sauransu, wasu suna cewa me yasa ba za ka baiwa wasu jaruman dama ba?”

Ali Nuhu: Wato abu daya da na sani shi ne tun da aka kafa masana’antar finafinan Hausa ba’a ta ba yin wani Darakta ba, wanda yake Promoting din jarumai maza da mata ba kamar ni, idan kuma  har za’a yi wannan korafin to akwai matsala kenan… domin akalla mata 12 zuwa 13 na yi promoting maza 9 zuwa 10 na yi promoting suka zama Jarumai. Sannan akan magana aiki kuma ya kamata mutane su gane ko a Fim din FKD ne idan ni Ali Nuhu bai dace da role din ba, ba za a saka shi ba, kwana nan nan na kammala wani sabon fim mai suna  ‘Bana Bakwai’ ka ganni a ciki? Babu ni a ciki saboda babu role din da zan yi a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *