Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu

Kungiyar Kwadago ta Jihar Kano ta bayyana cewa matukar Gwamnatin Jihar
Kano bata biya mata bukatunta ba nan da 15/6/2020 zata tafi yajin aikin gargadi na Makwanni biyu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Kungiyar na Jihar Kano Comrade Kabiru Ado Minjibir (Magayakin Minjibir) a wani taron manema labarai da Kungiyar ta kira a Sakateriyar Kungiyar Ma’aikatan lafiya ta Kasa reshen Jihar Kano dake Unguwa uku a yau Laraba 27/5/2020.

Shugaban ya lissafo bukatun kungiyar Guda 5 ciki har da mayarwa da duk wanda aka yankarwa Albashi kudinsa, da gyarawa Maaikatan Furamari, da na Kananan Hukumomi, da na Sharia da na Manyan Makarantu Albashinsu na mafi karancin Albashi na Dubu 30 daidai da yanda doka da tsara.

Sauran bukatun sun hada da samar da alawus ga Iyalan Maaikatan da suka kamu da cutar Covid-19, a kuma biya dukkan Maaikata Ariyas din su na karin Albashin da akayi, sannan a dakatar da yankewa dukkan Maaikatan Albashin nasu na take.

Shugaban yace wannan matsaya ta samu sa hannune da kungiyoyi Maaikata guda 13 na jihar Kano bayan sun kammala taron gaggawa, kuma sun bawa Gwamnati sati biyu, in har bata biya musu wadannan bukatuba, babu makawa zasu tsunduma yajin aiki na Gargadi na Makwanni 2, daga nan za su sake zama don tattauna hali na gaba in har ba a samu daidai to da Gwanmati ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *