Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu

Yanzu haka dai wani Matashi da ya shagaltu da daukar Hoto samfurin Salfie lokacin da yake zabga gudu akan Gadar sama.

Lamarin dai ya faru ne a daidai gadar Ibrahim Taiwo Road wajen yankura, Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa matashin ya karye a kafa, sannan kuma ya samu wasu raunuka a jikinsa.

Tuni dai yan kwana kwana da Jami’an ‘Yan sanda dake wannan waje suka dauke shi zuwa Asbitin Murtala domin ba shi taimakon gaggawa.

Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa cewa ya yi da zarar sun tattara bayanan za su sanar da halin da matsashin ke ciki.

Harkar daukar hoto dakanka a tsakanin matasa abu ne da ya mamaye al’umma har ana kallonsa waƴewa da burgewa, ba tare da la’akari shagaltuwar da ake samu ba.

Daukar hoto da kanka na da matukar haɗari a wasu wurare da lokutta, abin da ƴakamata a kiyaye kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *