Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta mayarwa da ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, martani bayan ya karyata zargin da take yi na cewa ya tura mutane da makamai su kori ma’aikatanta daga ofishin da hukumar NCC ta ba su.


A wata hira da tayi da SaharaReporters, Dabiri-Erewa ta zargi ministan da aika ‘yan bindiga da su karbe ofishinta a watan Fabrairu. Sai dai ministan ya karyata wannan zargi da take yi da kanshi ta shafinsa na Twitter, in da ya ce karya take zabga masa.


Tuni dai Abike ta hau shafinta na Twitter ta mayarwa da Pantami martani, inda ta bayyanawa ministan cewa a matsayinshi na malamin addinin Musulunci bai kamata yayi karya ba. A cewar ta rashin ganin darajar mata da yake da shi yayi yawa.


“Bai kamata Malamin addinin Musulunci yayi karya ba, kayi mini haka ne saboda ni mace ce. Rashin ganin darajar mata da kake yi yayi yawa, mu mance da abinda ya faru a watan Fabrairu. Amma ina so ka bayar da duka kayan ofishinmu.” Cewar ta.


Haka kuma ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter a safiyar ranar da aka kwace ofishin nasu da sunan ministan ne ya aiko.


Haka suka ci gaba da musayar kalamai a kafofin nasu wanda hakan ya baiwa mutane mamaki musamman a banaren Pantami don ba komai shi namiji ne da ya fita hankali da sanin abin da yakamata, bai kamata ya biye mata ba bayan kare kansa da ya yi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *