Spread the love

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga manoman Najeriya su dage wajen noma abinci a wannan shekara domin gwamnati ba ta da kudin shigo da abinci daga waje, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban Kasa bayan ya kammala sallar Idi, da ya yi a Aso Rock.

Ina fatan a samu damina mai albarka domin albarkatun gona su yi kyau su yalwata a bana. Ina kuma fatan manoma zasu koma gona su dukufa da aiki domin noma abincin da muke bukata a kasar nan. Domin kuwa babu kudin da zamu shigo da abinci daga waje. Dole mu noma abincin da zamu ci bana.

Tun kafin barkewar annobar coronavirus, Najeriya ta rufe iyakokin ta da wasu kasashen domin hana shigo da kayan abinci kamar su shinkafa, Kaji da man fetur.

A dalilin Korona kuma kasar ta rufe duka iyakokinta har ga mutane, amma duk da haka a kan hada baki da baragurbin Jami’an tsaro ana harkallar shigo da iren-iren wadannan kaya cikin kasar nan.

Farkon damina ya kankama an zaburar da manoma kar su yi wasa da wannan damar ta wannan lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *