Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana farincikinsa kan goyon bayan da jama’ar Sakkwato suka bayar a wannan lokacin na cutar Korona.

Gwamna a jawabinsa na barka da sallah ga al’ummar jihar ya ce dole in mika godiyata ga al’ummar jihar Sakkwato kan goyon bayan da suka bayar a wannan lokacin na annoba, akwai bukatar a daure da biyar sharudda da ka’idojin da aka gindaya na kariya da cutar Korona.

Tambuwal ya jinjinawa gwamnatin tarayya a matakan da take dauka na kare lafiyar mutanen kasa, amma dai akwai matukar bukatar daukar mataki ga masu tayar da kayar bai da suka addabi wasu kananan hukumomi a jihar Sakkwato, an rasa rayukka da yawa da lalata muhallan mutane ds dama, dubban jama’a sun nakasa a jiki da tattalin arziki.

Haka ma ya goddewa hukumomi da kamfanoni da suka taimaka ma jihar a yakin da take yi da annobar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *