Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu.

Gwamnatin jihar Kano ta dauki matakin rage albashin maaikata ba tare da wata sanarwa ba, tun a daren Alhamis ne dai gwamnatin ta fara biyan ma’aikata sai dai albashin ya zo da gibin kudade wanda ma’aikatan suka dinga korafi kan hakan.

Wasu ma’aikatan da aka sanya muryoyinsu sunce bayyana cewa ”Ni an an cire min 13,500” wata ta ce ”Ni an cire min dubu 11,500 a cikin albashina” wani ma’aikacin ya yace ”an cire min 25,500 babu gaira babu dalili.

Ma’aikatan da dama da aka zanta da su sun nuna takaicinsu suna masu cewa babban abin takaicin ma yadda gwamnati ta gaza sanar da su don shiryawa abin kamar yadda ta yi wa masu mukaman siyasa, a makon da ya gabata ne dai gwamnatin Kanon ta sanar da rage albashin masu mukaman siyasa, inda ta ce za ta rika biyansu rabin albashinsu.

Da ya ke zantawa da manema labarai Shugaban kungiyar kwadago ta jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce kungiyar za ta gabatar da taro da sauran gamayyar kungiyoyin kwadago don fidda matsaya akan yadda za su tinkari lamarin.

Sannan ya kara da cewa basu da masaniya ta kusa ko ta nesa akan rage albashin ma’aikata, don haka ya ce ma’aikta su yi wa kungiyoyinsu kyakkyawan zaton kwato masu hakkinsu.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin mai magana da yawon Gwamnan Kano abin ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *