Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ya yi Magana kan abubuwan da ke faruwa a kasar nan kan matakan da shugabanni ke dauka don kare rayukkan mutane amma wasu na kallon lamarin kamar rashin kishin addini ne wanda ba haka ba ne shugabanci yana da wuyar al’amari, “yakamata mu talakawa mu sani ba mu fi Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar son musulunci ba fa.”

Sadaukin Sakkwato ya yi wadannan kalamai ne a fadar Sarkin Yakin Binji lokacin rabon Zakka da tallafin kayan marayu da mabukata da gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar domin rabawa a gundumomi 86 na jihar, ya ce in wani na ganin sarkin musulmi ko gwamna Aminu Waziri Tambuwal sun yi wani abu na kuskure su mutane ne ka rokar masu Allah gafara, domin kuskure ba ganganci ba ne.

Ya nuna rashin jin dadinsa yanda mutane ba su yi wa shugabanninsu uzuri a cikin lamurran jagoranci wanda hakan bai kyautu ga mabiya ba.

A gundumar Kware da shugaban hukumar ya je don rabon kayan a wurin sun koka masa kan karancin masu wankin gawa mata a yankinsu, in da suke son hukumar ta samar da wani tsarin wayar da kan jama’a musamman mata su samu ilmin yanda ake wanke gawar mace bayan ta rasu.

Wakilin garin Kware Sarkin Dutsen Sarkin Musulmi ne ya sanar da hakan a fadar Sarkin Yamma Kware.   

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *