Jami’an  ‘yan sandan da ba ma’aikata ne a jihar Sakkwato ba sun tafi da sanannen malamin addini a jihar  Malam Bello Yabo a gidansa dake unguwar low-cost da karfe biyar na yamma a birnin Sakkwato kamar yadda wata majiya ta tabbatar.


Majiyar ta ce an zargi jami’an ‘yan sandan su taho ne daga Abuja suka tafi da malamin kan wani Wa’azi  da ya yi game da rufe mutane da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya yi in da malamin ya cacake shi kan tsarin, kenan ana zaton Malam ne ya sa a kama Malam a garin da baya mulki.

 
In har wannan zargin ya tabbata ya nuna Gwamnan Kaduna yana da karfi a gwamnatin nan da har zai iya sa a Kama wani a sananne a wajen jiharsa. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *