Spread the love

Shaikh Murtala Bello wani malami ne a Sakkwato ya ce Sallar Idi wajibi ce bisa ga karantarwar malamman musulunci magabata.

Malam Murtala a wurin karatunsa da ya sanya a turakarsa ta Facebook ya ce malamai magabata sun yi sabani kan Sallar Idi, wasu na ganinta Sunnah ce kamar irinsu Imam Malik da Imam Shafi’i.

Wasu malaman sun dauki Sallar fardu kifaya ce irinsu Imam Ahl Sunnah waljama’a.

Malaman da suka dauki Sallar Idi wajiba ce sun hada da Imam Abu Hanifa da Shaukani da Nasurudden Albani da sauransu.

A mahanga ta ilmi ana ganin ra’ayinsu ya fi Karfi saboda Manzon Allah ya ba da umarnin zuwa Idi, kuma an ba shi labarin an ga wata da rana ya ajiye Azumi a gobe ya fita Sallar Idi bai bari ta fadi ba, ga kuma yin rahusa in ta haduwarta da Sallar Jumu’a Wanda ya nuna wajabcinsu.

Ya Kara da cewar Sallar Idi wajiba ce duk wanda bai yi ta ba wani uzuri ya sabawa Manzon Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *