Daga Ibrahim Hamisu.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da samun karin mutum 5 masu dauke da cutar Corona wato Covid-19 a Jihar Kano a yau Laraba da karfe 11:47 na dare.

Wannan ta sa adadin wanda suka kamu da cutar a jihar Kano yanzu ya kama mutum 847 sannan kuma mutum 36 daga ciki sun rasu, sannan mutum 121 sun warke kuma an sallame su.

Ya zuwa yanzu dai masu dauke da cutar corona a Nigeriya sun kai 6677, wadanda suka warke kuwa mutum 1840, sai wadanda suka riga mu gidan gaskiya mutum 200.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *