Spread the love
Hajiya Ubaida Bello a lokacin da take tattaunawa da manema labarai bayan ta hannunta kayan ga wadanda za su amfana.

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.

Gwamnatin Jihar Sokoto karkashin Jagorancin Aminu Waziri Tambuwal, ta bayarda Tallafin buhuhuwan Shinkafa da Turanmen Atamfa ga Mutanen dake dauke da Cuta Mai karya garkuwar Jiki wato HIV a Jihar Sokoto.

Tallafin wanda Sakataren Gwamnatin Jiha Mallam Saidu Umar ( Malam Ubandoman Sokoto ) ya bayar ta hannun Mai baiwa gwamna shawara ta Musamman kan kula da hakkin dan Adam da kungiyoyi masu zaman kansu (Human Rights, NGO and Donor Agencies), Hajiya Ubaida Muhammad Bello ta hannunta Buhuhuwan Shinkafa 25Kg, guda Arba’in (40) da Kuma Atamfa turmi Sittin (60) ga mutanen.

Coordinator na Network Of People Living With HIV/AIDS In Nigeria ( NEPWHAN ) reshen Jihar Sokoto ne Kwamared Hussaini Muhammad Gwadabawa ne ya karbi kayan tallafin amadadin Al’ummomin dake dauke da Wannan Cutar domin rarrabawa.

Hajiya Ubaida ta bayyana cewa, Maigirma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayar da tallafin domin saukakawa wadannan bayin Allah harkokin lalurorin Sallah.

Ta ce wannan gwamnati ta al’umma ce su ne take yi wa hidima ba kuma wani jinsin mutane da za a ware a ba shi fifiko a cin gajiyar gwamnati kan haka gwamna ya raba irin wannan tallafin ga kowa.

“Dubi yanda ya yi wa marayu goma ta arziki ya ba su yadi da kudin dunki, ya juya kan tsofaffi da masu neman tallafi, a ba ka buhun abinci da 5000, ta hannun hukumar Zakka da wakafi ta jiha. Ya baiwa limamai da sarakuna da Matasa kowa da irin nasa tallafin. ” in ji Hajiya Ubaida.

Ta ce Sakkwatawa su gode Allah da suka samu gwamna mai tausayin al’ummarsa da son taimakawa talakawa da abubuwan da za su taimaki ratuwarsu duk da halin da ake ciki kan annobar Korona gwamna ya biya albashi kan Kari ba tare da ya yankewa kowane ma’aikaci sisin kwabo ba, sannan ya biyo mabukata da wannan alheri, wannan abu kam sai gwamnan talakawa.

Shima ana shi Jawabin ya yi godiya amadadin wadanda suka amfana da Wannan Tallafin.

Hussaini Gwadabawa ya yi godiya ta musamman ga Gwabnatin Jihar Sokoto da Maigirma Gwamna da mukarraban shi kan wannan Tallafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *