Cmrd Murtala St Sokoto.

An bayyana cewa yan ta’addan Boko haram sun isa garin Dapchi dake karamar hukumar Tumburawa a jihar Yobe ne cikin motocin yaki dacmisalin karfe 7 na yammacin Litinin.

Wani mazaunin garin, Bala Bukar, ya bayyana cewa yan ta’addan sun bankawa gidajen mutane wuta yayinda mutanen suka gudu daga muhallin domin ceton rayukansu.

Bukar ya ce tuni an tura jiragen yakin sojin sama cikin garin kuma Sojoji na kokarin kawar da su.

Yace: “Sojoji da yan ta’addan na musayar wuta yanzu. Yanzu haka da nike magana ana jefe-jefen bama-bamai.”

“Yan ta’addan sun kwace gari. Yawancin mazauna garin sun gudu.”

Wani mazaunin daban wanda ya gudu garin Baymari, ya ce har gidan Maigarin an kona.

Ya ce watanni biyar kenan da aka janye jami’an tsaro daga garin.

Garin Dapchi ta fara kaurin suna ne a ranar 19 ga Febrairu, 2018 da yan ta’addan ISWAP sukayi garkuwa da yan matan makarantan sakandare 117.

Yayinda biyar suka mutu a tsare, an samu ceto sauran illa Leah Sharibu wacce suka rike saboda ta ki bari addininta na kirista.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *