Daga Ibrahim Hamisu.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya amince a cigaba da Zirga Zirga a jihar Bauchi da kewaye, Wannan matakin ya baiwa ‘yan jihar samun damar gudanar da Sallar Idi da kuma bude masallatan Juma’a tare da zuwa coci ranar Lahadi ga mabiya addinin Kirista.

Sanata Bala Muhammad shi ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki da aka fara da karfe 11:30 na safiyar yau a dakin taro na barikin soji da ke Bauchi.


Gwamna Bala ya kuma amince cewa za’a yi Sallar Idi karama kamar yadda aka saba duk Shekara. ya shaida cewar janye dokar zai fara ne daga gobe Alhamis 21 ga watan nan da muke ciki.

Har ila yau, gwamnan ya shaida cewar makarantun jihar za su ci gaba da kasancewa a rufe, kana ya kuma tabbatar da haramta sana’ar Achaba kwata-kwata a jihar, ya kuma sanar da cewar za a yi feshin magani na musamman a wasu wurare.

Sannan ya ce janye dokar zai kuma yi aiki harda kananan hukumomin da ya sanya dokar kullewa kwanan nan, inda ya ce hakan ya biyo bayan cikar kwanaki 10 da wa’adinsu yayi na kullewar kwanakin da aka musu domin yaki da cutar.

A gefe daya, gwamna Bala Muhammad ya ce sun yi nasarar yaki da cutar ta fuskoki daban-daban, ya sanar da cewar jihar ta ci karfin cutar matuka kawo yanzu.
Masu ruwa da tsaki da suka hada da Malamai, Fastoci, sarakuna, da sauransu ne suka halacci wajen taron. Ya shawarci alummar jihar da su bi shawarwarin likitoci wajen Sanya Takunkumi da nisantar cinkoso da wanke hannu.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan Matakin, babban Limamin Bauchi, Malam Bala Ahmad Baban Inna ya gode wa gwamnan bisa daukar wannan Matakin na janye dokar da zai basu damar sallar Juma’a da na Idi lafiya tare da baiwa jama’a damar zirga-zirga na yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *