Spread the love

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma’a a jihar ‘Allah ya isa’.

Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga ‘yan jiharsa a yammacin Talata.

A cewarsa, “Ko a makka ba za a yi sallar idi ba amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah.

Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni amma ba zan yafe wa wanda yayi min kazafi ba.”

Gwamnan ya bayyana ba su kadai ne suka hana yin Sallar Jumu’a da Idi ba Makka ma ta yi hakan duk abin da zai Kare al’ummarsa shi zai yi shi ko da wasu za su soke shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *