Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu

Baya ga wa’adin da gwamnatin taryya ta kara na zaman gida ga alummar Jihar Kano na sati 2, Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje shi ma ya yi wa dokar gyaran fuska ta hannun mai magana da yawunsa Salihu Tanko Yakasai

Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da shawarwarin wakilan malamai su 30 na jihar Kano daga bangare daban daban akan bada izinin yin Sallar Jumaah da kuma Idi.

Gwamna Ganduje ya bada wannan umarnin bayan tattaunawa mai tsawo da yayi da shi da Mataimakin sa da sauran jami’an Gwamnati tare da wakilam Malaman su 30 a dakin taro na Africa House a yanmacin yau.


Saboda haka za’a ci gaba da dage dokar hana zirga zirga ranakun Litinin

Laraba, da Jumu’a sannan kuma yanzu Gwamnati ta kara da bada izinin sallar Jumaah, sai kuma salllar Idi wadda ita ma aka yadda ayi ta sai dai banda shagulgulan Sallah.

Sannan an umarci Malaman Masallatan Jumaah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso.

Gwamnatin jiha ta kuma kafa Kwamaiti da zai lura da raba kayan tsaftace muhalli da Takunkumin fuska da sauran su ga masallatan jumaah na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *