Spread the love

TALLAFIN GWAMNATIN TARAYYA NA CORONA YA ISA KANO

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin Ministan agaji da jinkan alumma wato Honarabul Sadiya Umar Farouk wacce ta zo jihar Kano domin mika gudunmawar gwamnatin tarayya na motar Tirela 130 makare da kayan abinci.

Kayan abinci da suka hada da Shinkafa da Gero da Masara ga jihar Kano domin a rabawa masu karamin karfi wadanda ke da bukata musamman a wannan yanayi na tabarbarewar tattalin arziki saboda dokar hana zirga zirga wadda wannan ta hana mutane zuwa wajen aiyukan su domin neman abinda za su ci.

Ministar ta zanta da gwamnan a fadar gwamnatin jiha kafin mika kayan abincin da wasu ke ganin ya kamata a mika su ga jihar tun kafin yanzu.

Ganin yanda gwamnan ya yi ta Kira ga gwamnatin tarayyar da ta kawowa jihar daukin gaggawa kan halin da suke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *