Spread the love

Daga Murtala ST Sokoto.

Kungiyar matasa masu Rajin kawo zaman lafiya a cikin al’umma da ake kira “Youth for Resolution and Peace Building Initiative”,ta gudanar da cin abincin buda bakin azumi tare da membobin kungiyar Kiristoci reshen jihar Sakkwato.

Shugaban kungiyar a matakin kasa, Kwamared Abarshi Salman ya bayyana cewa kungiyar ta shirya wannan buda bakin ne tare da gayyato kungiyoyin addinin kirista domin su yi  addu’ar samun zaman lafiya a kan matsalar tsaro dake addabar sassan kasar Nijeriya, da yin addu’oin samun sauki annobar korona da ta addabi kasar nan da duniya baki daya.

Ya bayyana cewa anan gaba kadan kungiyar za ta sake shirya wani taron samun fahimtar juna ta hanyar tattaunawa a tsakanin addinai daban-daban  domin samun bayanai da fahimtar juna ga addinan guda biyu Musulunci da Kiristanci.

Sarkin yakin Gagi Alhaji Sani Umar Jabbi,ya yabawa kungiyar akan irin zurfin tunanin da ta yi na gayyato bangaren  addinin kirista domin Shan ruwa tare da su,  wannan shi ne ya nuna cewa akwai kyakyawar fahimtar tsakanin mabiya addinan biyu a jihar nan, ya Kuma Kara tabbartar da  tarihin da jihar Sokoto ke da shi na zaman lafiya.

A saboda haka ya nemi kungiyar ta cigaba da hada Kai tsakanin bangarorin daban daban idan tana son ta karbi sunanta a matsayin kungiyar da ke son kawo sulhu a tsakanin Al’umma.

Da yake mayar da jawabi shugaban kungiyar kiristoci  reshen jihar Sokoto(CAN) Rabaren Nomau,ya godewa kungiyar akan tunanin gayyato kungiyar su domin Shan ruwa tare, da Kuma Kara jinjina musu wajen wayar da Kai a Kai akan lamurra daban daban.

Haka ma ya yi alkawalin samun hadin Kai tsakaninsu da kungiyar domin samun zaman lafiya a jihar Sokoto da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *