Spread the love

Jaridar Taskar Labarai dake Katsina ta ruwaito cewa ‘yan sa kai sun kashe wata mata mai suna Abu wadda uwar daba ce babba a garin Yankara ta karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina.

Matar mai suna Abu tana da ‘ya’ya masu yawa kuma ana zargin yawancinsu duk barayi ne.

‘Yan garin sun ce wani dan Abun ne ake zargin sun kashe wani mai mashin suka kwace babur dinshi, kuma wasu sun ga lokacin da suka yi, sai jama’a suka ganshi cikin gari, suka kama shi suka mika ma ‘yansanda.

Abu tana jin labarin cewa an kama danta an baiwa ‘yansanda sai ta zo cikin garin Yankara daga Rugar da take zaune, ta yi gargadin cewa, a sako mata danta ko kuma Yankara ta gama zama lafiya.

Jin wannan kalaman na Abu ne ake zargin ‘yan banga suka kamata suka kai ta wajen gari suka halaka ta. Kamar yadda ake yawo da hotonta a kafar Sada zumunta.

An ce Fulanin sun ji haushin kisan Abu kuma sun sha alwashin daukar fansa duk rumtsi.

Tun a yammacin juma’a Fulanin suka taru da yawa a bayan garin na Yankara da sunan sun zo daukar gawar Abu ne da aka kashe suna kuma neman shigowa.

Amma jami’an tsaron dake cikin gari da shirin kota kwana na ‘yan banga Sun hana su shigowa.

Wata majiyar ta ce Fulanin sama da dari sun dauki gawar Abu suka shiga da ita daji, don yi mata sutura, wani ya fada cewa suna kuka da shan alwashi suka tafi da gawar daji.

Wani da ya san tasirin Abu a wajen Fulanin ya ce, sun dauke ta uwa ne, kuma ‘ya’yanta manyan kwamandojinsu ne, hatta wasu manyan kwamandojin dake wasu shiyyoyin suna kai mata gaisuwa.

Wani jirgin soja yazo ya taimaka ma sojan kasa da ‘yan banga suka kora fulanin cikin daji, suka kuma hana su shigowa garin na yankara.

Fulanin sun ajiye ‘yan sa ido wajen karfe Goma na dare, soja suka bar garin Yankara, suna bari da minti Goma, Fulanin suka shigo garin. A wata majiyar.

Ita kuma wata majiyar ta ce Sun bi duk gidan wani dan banga da suka sani, wanda duk sun bar gidajensu, sun kashe mutane biyu da suka iya samu. Sun kona wasu gidajen suka kuma fasa shaguna da dibar kaya.

Wani da ya boye, a saman kwanon wani gida ya fada wa Taskar Labarai cewa da kunnensa yaji wasu na cewa daukar fansa Abu dole ne, suna fadar cewa wane da wane sun bugo waya daga daji kaza suna jajantawa.

Daidai rubuta labarin nan, da yawa daga mutanen garin Yankara sun kaurace ma garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *