Spread the love

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal.

  Hukumar bayar da agaji gaggawa ta Jihar Sakkwato a karkashin jagoranci  mai ba  gwamna shawara a hukumar  Honarabul Zubairu Albadau ta raba kayan masarufi ga ‘yan gudun hijira na garin gandi dake jihar Sakkwato don kara saukaka masu a wannan watan na Azumin Ramadana.

Ya jagoranchi ba da tallafi kayan abinci wadan da suka hada da shinkafa, gero,  shanu, da shadodi da atamfa ga ‘yan gudun hijira a garin gandi cikin Karamar hukumar Mulkin Rabah a jihar Sakkwato.

Sakataren  Gwamnati Jihar Sakkwato Malam Saidu Umar  (Malam Ubandoma Sokoto) Shi ne ya Wakilci Mai Girma gwamna jihar Sakkwato  Aminu Waziri Tambuwal a wurin rabon  ya yi kira ga wadan da suka samu kayan su tafiyar da su yanda yakamata, domin a saukaka masu halin rayuwa ne aka yi masu wannan goma ta arzikin, gwamnatin Sakkwato ba ta da burin da ya wuce ta kyautatawa mutanen jihar domin samun romon dimukuradiyya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *