Spread the love


Daga Ibrahim Hamisu

Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da rabon safar baki da hanci ko takunkumin fuska wato (face mask) guda Miliyan 2 wanda zaa raba a fadin jihar Kano baki daya.

Gwamnatin jiha ce ta samar da guda Miliyan1  sai kuma gamayyar kananan  hukumomi na jihar Kano 44 su kuma suka samar da guda miliyan 1.

Sannan kungiyar teloli ita ma tana ci gaba da dinka na ta wanda nan gaba za’a raba su. 


Gwamnatin jihar Kano ta maida saka safar fuska wato ( face mask)ya zama dole a jihar Kano domin kare kai daga kamuwa daga cutar Corona wato Covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *