Spread the love

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sakkwato, ya samarwa wasu matasa masu  zaman fursuna 31 ‘yanci daga gidan yarin Sakkwato.

Matasan sun samu damar walwala ne biyowa bayan biya musu tara da gidauniyar Aliyu Magatakarda a fannin shari’a ta yi musu.

Sakataren gidauniyar Barista Bashir Jodi ya bayyana cewa masu zaman fursunan an biya musu bashin dake tattare a kan su, wanda shi ne silar zamansu gidan yarin.

Ya Kara da cewa, dukkan mutanen maza ne Kuma an baiwa kowanen su naira dubu biyar na mota domin Kama hanya zuwa gida.

Barista Jodi ya ce, wannan na daga cikin irin karimcin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na taimakawa marasa karfi Musamman a lokacin watan Ramadan domin su Sami damar yin lalurorin sallar idi tare da Iyalansu.

Shi kuwa mataiamakin Shugaban Gidan yarin Mai kula da ajiye fursunonin a Jihar Sakkwato, Idris Muhammad ya yabawa kokarin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan wannan karimcin.

Ya Kuma yi Kira ga masu abin Hannun su a cikin Al’umma da su yi koyi da wannan kwazon na Sanata Wamakko domin taimakawa marasa karfi cikin Al’umma.

Malam Idris ya Kara da cewa, wannan karimcin da cewa abu ne da yazo daidai lokaci kasancewar Duniya na fuskantar matsalar murar mashako ta Coronavirus.

Ya ce kuma wannan karimcin ya taimaka ainun ga Gidan yarin ta bangaren sha’anin tsaro domin kuwa za a Sami ragowar masu laifin dake Gidan yarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *