Spread the love

Daga Zaharaddeen Gandu.

 Kusan kwana uku kenan a jere babu ranar da barayi  ba sa kashe mutum daya ko biyu a garin ‘Yankara dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Bayan an sha ruwa na yi ta ganin sakonni ta inbox (akwatin sakonni) dina na shafin hanyar sadarwa ta Facebook, inda wani dan yayata Mustapha ‘Yankara yake ce min “Bayan an sha ruwa barayi sun yi wa garin ‘Yankara zobe, suna ta harbe-harbe, domin shi ma a boye yake a wani gidan yayan abokinsa, yanzu haka gidansu babu kowa”.

Bayan na gama karanta sakonsa kamar na yi kuka, zuwa can sai mamarsa Saratu Zayyana wadda yayata ce uwa daya uba daya, ta kira ni cikin murya kasa-kasa take cewa “Zaharaddeen mun shiga uku, barayi sun shigo garinmu suna ta harbe-harbe, yanzu haka a boye nake wannan wayar, gashi kuma dare na yi, saidai ku taya mu da addu’ar Allah ya kubutar da mu”.

Bayan na gama waya da ita, sai mijinta Alhaji. Muntari ya kira yayana Alhaji Abdullahi Zayyana ya ke ce mishi “Wallahi tallahi garinmu ba lafiya yanzu haka gidana ba kowa ban san inda kowa yake ba, kowa ya gudu yana neman inda zai tsira”.

Ya Allah ka taimaki talakawa, ka kare su daga wannan masifun dake afka musu, gashi gwamnatin ta kasa ba su tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *