Spread the love

Daga Muhammad kwairi waziri 

Gwamnatin Nijeriya ta yi gargaɗi gamutanen da suka warke daga cutar Korona barus su daina bayar da cikakkun bayanai kan magungunan da suka sha har suka warke, don kada mutane su dinga yin gaban kansu.


Sakataren gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaƙi da cutar korona Boss Mustapha ne ya bayyana haka a taron manema labarai game da halin da ake ciki kan matakan da gwamnati ke ɗauka na daƙile cutar a Najeriya.


Ya ce wasu da suka warke kuma aka sallame su, sun fito suna bayyana irin magungunan da aka ba su wanda a cewarsa zai sa waɗanda ke fama da cutar korona su dinga saye suna sha ba tare da shawarar likita ba.


Ya ƙara yin kira ga duk wanda ya ji alamomin cutar korona ya yi gwaji, ko ya kai kansa ɗaya daga cikin cibiyoyin killace masu dauke da cutar korona domin samun kula ta musamman.


Ya ce magance alamomin cutar ya sha bamban da magance cutar baki ɗaya, don haka suke yin kira a guje wa shan magani ba tare da shawarar likita ba.

Amma wasu na kallon wannan matakin kamar wani abu ne boyayyen lamari da ake ki tsawa da mutanen kasa ba su san in da aka dosa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *