Spread the love

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya yiwa kasafin shekarar nan ta 2020 kwaskwarima, sakamakon bullar cutar Korona a duniya, wadda ta kawo cikas ga tattalin arzikin Nijeriya da kuma jihar katsina. 


Hakan  ya tilastawa jihar Katsina zaftare kiyasin kasafinta, har na naira miliyan dubu talatin da daya(31b). 


Gwamna ya bayyana cewa ragewa ta zama dole sakamakon fuduwar gangar danyen Mai a duniya.


Masari ya bayyana haka ne, a lokacin da yake sanyawa kasafin kudin wanda aka yiwa kwaskwarima, da ya aike da shi a majalisar dokoki ta jihar Katsina, wanda majalisar ta kammala gyaran, aka maido ma gwamnan domin sanya mashi hannu ya zama doka Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada. 

Masari ya kara da cewa ” wannan shi ne karon farko a cikin shekara biyar da ya zama dole mu sassake wasu ayyuka da muka kudiri aniyar yi a jihar Katsina, a cikin wannan shekara da muke ciki da kashi talatin. Sakamakon bullar wannan annoba ta Korana, wadda ta shafi tattalin arzikin jihar Katsina. 


Gwamnatin Tarayya ta rage kiyasin kudin gangar danyan Mai daga dalar Amurka hamsin da bakwai zuwa dalar Amurka talatin, wadda ya shafi kudin shigar mu daga asusun da muke samo kudin daga Gwamnatin Tarayya. Muna fata da cigaba da adduar wajen Allah madaukakin sarki, kar abun ya cigaba da runcabewa, saboda idan farashin ya cigaba da saukowa zuwa dalar Amurka ashirin, za mu kara shiga wata matsalar.


Gwamna Masari ya cigaba da cewa mun yi kiyasi kasafin kudin naira biliyan dari biyu da arba’in da hudu, amma yanzu mun yi masa kwaskwarima zuwa biliyan dari biyu da sha ukku. An zaftare naira biliyan talatin da daya. Da ni da yan majalisun jihar Katsina, mun duba bangaren manyan ayyuka da kuma ayyukan yau da kullum. Ayyukan yau da kullum kamar biyan albashi da biyan fansho ba mu taba su ba.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yaba da yadda ‘yan majalisun suka gudanar da aikin cikin sauri kuma cikin lokaci. 


Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Katsina su zamanto masu bin shawarwarin masana kan wannan annoba ta Korana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *