Spread the love

 

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto.

Uwargidan Gwamnan jihar Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal takaddamar da rabon kayan abinci ga wasu marasa galihu  a jihar Sokoto. 

 Mutum 20 maza da Mata wadanda aka zabo a wasu manyan hanyoyin birnin  sokoto, mafiyawancinsu masu tsananin bukata ne, an yi haka ne domin faranta masu rai a halin da ake ciki.

A wurin rabon uwar gidan Gwamnan ta ce sun yi wannan aikin ne ta kungiyarsu ta matan gwamnonin Arewa domin su saukaka wa almumma radadin annobar korona  ga kuma yanayin  Azumi.

Ta kuma yi Kira ga al’umma da su bi shawarwarin masana kan Kare Kai ga cutar korona.

Shugaban Hukumar zakka da wakafi ta jihar Sokoto Malam muhammad Lawal Maidoki ya  ce  wadanda suka amfana da tallafin awa biyu da suka wuce ba su san za su samu wannan tallafin ba,” da sakon bayar da tallafin ya zo muna kawai mun bi wasu manyan tituna ne na cikin birnin Sokoto, muka zakulo mabukatan, wasu a wajen baransu muka gansu, wasu suna wajen sana’arsu.” A cewar Sadaukin Sakkwato.

Shugaban ya yabawa matar gwaman da kungiyarsu kan yin wannan aikin cikin wannan lokacin, ya yi Kira ga wadanda suka amfana da su yi amfani da tallafin ta yadda ya kamata.

“ku yi ja Jarin sana’a  Mai makon bara, mun zakulo ku ne domin kun cancanta ba mu baiwa wadan da ba su cancanta ba.” In ji Mai doki.

Honarabul  Fatima Khalil ce ta hannunta sauran kayan madadin asusun uwar gidan gwaman dan rabawa ga sauran mabukata.

Kayan da aka raba su hada da Gero, masara, taliya, Shinkafa da kudin sufuri domin kai kayan gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *