Spread the love

Majalisar Koli ta harkokin addinin musulunci a Nijeriya da malalisar musulman Nijeriya sun yi kira ga musulman Nijeriya su gudanar da addu’o’i a Alhamis(yau) domin ganin an kawo karshen musibar annobar Korona, a roki Allah ga dukkan kalmomin da an ka sani.

Wannan kiran ya zo ne bayan matsayar da babban kwamitin al’umma dake tafiya tare, wanda shi ne koli a harkokin addini a duniya ya cimma.

Babban malami a Azhar Al-sharif da takwaransa Fafuroma Francis fada a cocin Vatican su ne suka yi wannan kiran cewa mabiya addinai daban-daban su yi addu’o’i a duniya gaba daya.

A bayanan da aka fitar a jiya Laraba wanda shugaban kwamitin fatawa na majalisar koli a harkokin addinin musulunci a Nijeriya Shaikh Shariff Ibrahim Saleh ya fitar ya ce sakataren majalisar dunkin duniya ya goyi bayan wannan kyakkyawar manufa, kamar mafiyawan malaman musulunci da jagororinsu a fadin duniya.

Shaikh ya ce kamar yadda karantawar addini ta zo an zaburar da musulmai su yi addu’a a duk lokacin da suke cikin musibu da rikici da duk wasu miyagun kaddarori dake fadawa mutane a kowane lokaci.

Ya ce amadadin kwamitin Fatawa kan shawarar da sarkin musulmi ya bayar suna kira ga al’ummar musulmi da kiristoci da abokai da masoya a duk in da suke da su yi addu’a da murya daya a ranar 14 ga watan Mayu 2020, domin Allah Ya kawar da wannan musibar da ake ciki.

Ya ce wannan abu ne mai kyau, sunnah ce ta manzon Allah yana fita rokon ruwa, yakan zaburar da kowa ya je wurin addu’ar ba tare da la’akari da shekarru da bambancin addini ba.

Managarciya ba ta samu kwafin bayanin ba, sai dai ta kalato wannan labari ga wata jaridar turanci, don ta so ta sani shin ana nufin a hadu wuri daya a gudanar da addu’o’in ko dai a gida kowa zai yin tasa, ganin yanda aka ce a yi da murya daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *