Spread the love

Allah ya yi wa Alhaji Daudu Ahmed Galadanci rasuwa,(Alkalin Kuliya). Za a yi jana’izarsa yau Alhamis da karfe 9:00 na safe a Unguwarsu ta Galadanci.

Kafin rasuwarsa, ana kyautata zaton babu ɗan wasan da ya kai tsufansa ko daɗewa a harkar wasan kwaikwayo na Hausa.

Tun ana wasan daɓe ya fara dirama, har aka zo ana nuna su a talbijin, inda ya riƙa fitowa a matsayin alƙali a shirin ‘Ƙauliya Manta Sabo’, inda ya samo laƙabin sa na Ƙuliya, har kuma zamanin finafinan Hausa na Kannywood ya shigo, inda aka dama da shi tsawon lokaci.

Yakan fito Basarake ko kaka a finafinnan Hausa kafin rasuwarsa an daina ganinsa a cikin finafinnan abin da ake ganin ya jingine su domin shekarru sun ja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *