Spread the love

Wasu daga cikin matan da kungiyar ta horas da su sana’o’in hannun mata a lokacin suna karbar horo.

Shugaban kungiyar Sahihiyar rayuwa ta al’umma da matasa a jihar Kebbi Malam Sharhabilu Muhammad Sani a zantawarsa da Managarciya a satin da ya gabata a ofishinsa dake birnin Kebbi ya bayyana dalilinsa na kafa kungiyar domin a samu a kawar da kalubalen da matasa ke fuskanta dake jefa su a cikin aiyukkan dabanci da shaye-shaye.

Ya ce saboda canja tunanin matasa da samar da aiyukkan yi gare su ya sa muka assasa wannan kungiyar ta magance zaman banza ta kuma baiwa ilmin mata muhimmanci musamman a jihar Kebbi.

Sharhabilu ya ce kafin shigowar cutar Korona sun yaye dalibai maza da mata 3000, amma daga kafa kungiyar a 2014 zuwa yau 2020 sama da dubu 17 ne suka koyi sana’o’in hannu daban daban a dukkan kananan  hukumomin jihar Kebbi 21.

Ya juya kan maganar in da suke samun kudin gudanar da horas da matasan ya ce suna samun kudin ne ta hanyar sayar da fom da kuma sayen abin karatu, ta hakan ake tafiyar da horaswa daga farko har karshe, kuma akwai wasu ‘yan kasuwa masu kishin jiha dake daukar nauyin wani yankin matasan tun da suka fara har zuwa yau.  

Ya bayyana bunkasar kungiyar kan jajircewar duk wadan da suke cikin kungiyoyin a kananan hukumomin jihar musamman masu bayar da horaswa da ba biyansu ake yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *