Spread the love

Sanannen a harkar finafinnan Hausa Ali Nuhu ya ce ya daina sumbata ko rungumar mata a finafinan kudancin Nijeriya ne saboda hakan bai dace da al’ada da addininsa ba.

A hirarsa da BBC a shafin Instagram ranar Talata, shahararren dan wasan na fina-finai ya ce ba zai daina sana’ar fim ba.


Da yake amsa tamabayar da wani mai sauraronmu ya yi masa kan yadda yake fuskantar yanayin da zai iya kai shi ga runguma ko sumbatar mace a finafinan Nollywood, Ali Nuhu ya ce “a shekarun baya idan ka lura na yi irin wadannan finafinai amma daga baya da na ga korafe-korafen mutane, ka ga mutum jakada  na Arewa kuma Musulmi, shi ya sa ni yanzu ba na fitowa a irin wadannan fim din.”

Ali Nuhu ya ce babu wanda ya taimake shi da ko sisi lokacin da zai soma shirya fim.
A cewarsa, ba zai iya kayyade adadin fina-finan da ya fito a cikinsu ba saboda yawansu, yana mai cewa wasu daga cikin su ma ana sauya musu suna kafin su fito don haka ba zai iya rike sunayensu ba.


Rayuwar Ali Nuhu a takaice
An haife shi a watan Maris na 1974
Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
Ya yi digiri a jami’ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo a 1999.


Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a finafinna Turanci na kudancin Nijeriya waton Nollywood, ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya.


Ya ci lambobin yabo da dama, ya kuma yaye matasa sosai a masana’antar abin da ya sa ake masa lakabi da Sarki,
Tauraron wanda ake yi wa lakabi da Sarki a fagen fina-finan Kannywood, ya ce harkar fim ce abin da ya fi sani a rayuwarsa tun yana matashi har yanzu don haka babban burinsa shi ne ya ga an ci gaba da samun sauyi mai kyau a masana’antun fina-finai.

Ali Nuhu dai ya kwashe fiye da shekara 20 yana taka rawa a fina-finan Kannywood da Nollywood, inda ya lashe lambobin yabo a ciki da wajen Nijeriya.


Kusan shi kadai ne tauraron da ya kasa dusashewa a masana’antar koyaushe za ka ana yayinsa duk yana haska sabbin Matasa a harkar amma ba su yi wa tashensa komi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *