Spread the love


Kungiyar masu gidajen sayar da man fetur ta Najeriya PETROAN ta koka kan abin da gwamnati ta yi na rage kudin da take basu mai amma bata rage kudin da za’a rika sayar da man ba a gidajen man.


Gwamnati ta hannun kamfanin mai na kasa, NNPC wanda shi ne babban me shigo da mai kasarnan ta bayyana ragin kudin da take baiwa masu gidajen mai daga 113.28 zuwa 108. Saidai bata bayyana nawa za’a rika sayar da man a gidajen mai ba.


NNPC ba ita ce ke da alhakin bayyana kudin farashin sayar da mai a gidajen mai, ba PPPRA ce ke da wannan alhakin. Kuma duk da cewa ta yi alkawarin rika bayar da farashin mai a kowane wata amma gashi an yi nisa a watan Mayu, bata ce komai ba.


Hakan yasa shugaban kungiyar ta PETROAN, Billy Gillis-Harry ya bayyana cewa gwamnatin na so ta hadasu fada da ‘yan Najeriya.


 Yace gwamnati ta rage kudin da take basu mai daga 113 zuwa 108 kan kowace ganga amma bata bayyana nawa zasu rika sayarwa da mutane ba. Yace idan mutum ya zo sayen mai yasa suna sayarwa a farashin 125 kan kowace lita zai iya musu tambaya kan ragin da aka yi.


 Yace rashin bayyana farashin da zasu rika sayar da man na nuni da cewa gwamnati ta basu damar sayar dashi duk yanda suka ga dama kenan.


Ya ce sun yi magana da hukumar dake da hakkin kayyade farashin ta PPRA amma har yanzu babu wani abu da aka cimmawa.


Saidai yace har yanzu fa akwai wanda ke da man da suka siyo a tsohon farashi dan haka ba lallai a fara ganin canji ba sai sun kammala sayar da shi.


Masu gidajen man da kara kudin Mai aka yi ba su jiran gwamnati za su Kara kudin amma yanzu tun da ragi ne suna jira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *