Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta ce ta kama ‘yan kasar China biyu bisa zargin yunkurin bai wa jami’inta cin hanci.

A taron manema labarai da shugaban yankin Abdullahi Lawal ya kira  ya ce jami’ansu sun kama Mista Meng Wei Kun da Mista Xu Koi a unguwar Kasarwa a Sokoto bisa zargin bai wa shugabanta reshen yankin Sokoto Abdullahi Lawal, cin hancin miliyan 50 a cikin yarjejeniyar da suka yi za su bashi miliyan 100 toshiyar baki.


A cewar EFCC, mutanen biyu sun bayar da cin hancin ne domin su hana binciken da ake gudanarwa kan kamfanin gine-gine na China Zhonghao Nig. Ltd, wanda gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa kwangilar da ta kai  biliyan 55 tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.


Shugaban hukumar reshen jihar Sokoto yana binciken kamfanin ne game da aiwatar da kwangilolin gina hanyoyi a garuruwan Gummi, Bukkuyun, Anka da kuma Nassarawa dake jihar ta Zamfara; da kuma haƙa rijiyoyi 168 masu amfani da hasken rana a kananan hukumomi 14.


EFCC ta ce ‘yan kasar ta China sun razana ne saboda yadda suka ga shugaban hukumar reshen jihar ta Sokoto yana gudanar da aikinsa ba sani ba saboda, abin da ya sa suka nemi ba shi cin hancin miliyan 100.


Daga nan ne,  Lawal ya yi musu ƙofar-rago inda ranar Litinin wakilan kamfanin biyu Meng Wei Kun da Xu Kuoi suka ba shi miliyan 50 a matsayin kashin farko na cin hanci.


EFCC ta soma binciken kamfanin ne bayan da a cewar ta, bayanan sirri suka nuna cewa an yi almubazzaranci da kudin da kuma halasta kudaden haramun lokacin bayar da kwangilar.


Binciken ya gano cewa kamfanin na China Zounghao Ltd ya karbi biliyan 41 daga gwamnatin jihar Zamfara kuma an karkatar da biliyan 16.


Hukumar ta EFCC ta ce nan gaba kadan za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu kan laifin da suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *