Jihar sakkwato ta yi rashin wasu muhimman mutane   a rana daya  sakamon fama da rashin lafiya.

Dakta  Haliru Alhassan shi ne tsohon Ministan Lafiya a Tarayyar Najeriya a zamanin mulkin shugaban kasa Goodluck Johnathan, ya rasu yana shekara 65 da mata daya da yara hudu.Ya yi fama da ciwon suga wanda shi ne ya zama a jalinsa.

Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya rasa kwamishinansa na gidaje da filaye  Honarabul Sirajo Marafa Gatawa, ya ba da sanarwar rasuwar da marecen Lahadi.

Kwamishinan wanda ya rasa ransa bayan gajeruwar rashin lafiya an haife shi a garin Gatawa a shekarar 1957, ya taba zama kansila a karamar hukumar Sabon Birni kuma ya zama shugaban karamar hukumar,daga bisani ya zama dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan  hukumomin Isa da Sabon Birni daga 1999 zuwa 2007.

A wa’adin mulkin Tambuwal na farko ya nada shi kwamishinan jindadin jama’a, da ya dawo wa’adi na biyu ya tura shi a in da yake yanzu har rayuwata yi halinta.

Margayi Gatawa ya bar matan aure uku da ‘ya’ya da dama, an yi masa sutura kamar yadda addini ya tanada.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *