Spread the love

Kungiyar ‘yan jarida masu aika labari waje waton correspondents a Lahadin nan ta yi ta’aziya ga gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kan rashin kawunsa Shaikh Haruna Waziri Usman.

Margayin ya rasu a garin Tambuwal da shekarru 96, a sakon ta’aziya da shugaban kungiyar da Sakatarensa Habibu Harisu da Ankeli Emmanuel suka sanyawa hannu sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar ga irin gudunmuwar da ya bayar ta ilmi da cigaban al’umma.

“Waziri Usman Sanannen malami ne da ya karantar da al’umma sanin Allah da kyawawan hali domin samun rabauta.” kamar yadda bayanin ya ce.

Kungiyar ta roki Allah ya gafartawa mamacin ya baiwa dangin Wazirin Tambuwal hakurin jure rashin mamacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *