Spread the love

Allah Ya yi wa Sheikh Adamu Muhammad Gashuwa rasuwa, daya daga cikin manyan malaman Kungiyar jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatus Sunnah mai hidikwata a Jos.

Malam Adamu Muhammad Gashuwa babu shakka an yi babban rashin Malami masanin fannoni na addini kuma tsayayyen namiji.

Ya bar babban gibi a Kungiyar da jiharsa ta Yobe da garinsa na Gashuwa, domin mutum ne da ya yi fice a wajen fadin gaskiya da son jama’a a jikinsa da ba ruwansa da harkokin ‘yan siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *