Spread the love


Kungiyar Kimaman Kano ta nemi gwamnatin jihar da ta sanar da ita matsayinta kan sallar Idin karamar sallah, shin zata samu yi ko kuwa a’a?


 A yanzu haka dai gwamnatocin jihohi sun kulle garuruwansu inda aka hana tarukan Ibada dana bukukuwa kuma mafi yawanci ana zaune a gida saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 da har yanzu ba’a gano rigakafi ko maganinta ba.


Shugaban kungiyar Limaman,Sheikh Ibrahim Khalil ne ya bayyana haka bayan wani taro da kungiyar ta yi, ya ce mabiyansu nata ta tambayarsu shin za’a samu yin sallar Idi kuwa? Shiyasa suke son amsar wannan tambaya dan su san abinda zasu gaya musu.


Ya kuma kara da cewa, membobinsu sun nuna rashin jin dadinsu kan yanda gwamnati a damar data bayar na kwanaki 2 a rika fita Kasuwa, watau Alhamis da Litinin amma bata duba maganar Sallar Juma’a ba.


Ya kuma yi kira ga gwamnati data yi bincike kan yawan mace-macen da ake samu a jihar dan sabbabinsu saboda a kore fargabar dake zukatan mutane.


Bullar cutar na Kara yawa a jihar in da a yanzu ta gaban Abuja. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *