Spread the love


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziya ga gwamnatin jihar Sakkwato da al’umma kan rasuwar Shaikh Waziri Usman Mai shekarru 96 bayan ya yi doguwar jinya.  


A bayanin da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ya ce jihar Sakkwato da kasa baki daya sun rasa babban malami. 


Sheikh Usman yana cikin dangin Wazirin  Tambuwal kawu ne ga gwamnan Sokoto  Aminu Waziri  Tambuwal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *