Amaryar da aka sace ana saura kwana biyu bikinta a kai ta dakin miji ta kubuta bayan ta yi sati uku hannun masu garkuwa

Khadija Nasir Yankara da aka sace tare da babbar kawarta ana saura kwana biyu bikinta, ta kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan ta share sati uku a hannunsu, sai dai ba a bayyana yanda ta kubutar ba.

Za a iya tuna cewa Katsina Daily Post News ta rawaito cewa tun da farko  an shiraya za a yi bikin  a ranar 18 Afirilun daya gabata, ‘yan bindiga suka shiga gidan mahaifinta a garin Yankara ta karamar hukumar Faskari inda suka sace ta tare da kawarta ranar Alhamis 16 ga watan Afirilun din da ya gabata a wannan shekara ta 2020.

Ta kubuta ne a yau tare da sauran wadanda aka yi garkuwa tare da ita tare da su.

Managarciya za ta ba mu sauran bayanin daga baya da zaran an samu Karin bayanin yanda suka kubuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *