Spread the love

Jam’iyar PDP a Nijeriya ta yi watsi da kudirin gwamnatin tarayya kan sabon farashin man fetur da ake son ya dawo 108, farashin kamata ya yi ya dawo naira 60 ko 70 ganin yanda farashin danyen man fetur ya fadi warwas a kasuwar duniya.

Sakataren yada labaran jam’iyar Kola Ologbodiyan ne ya fitar da bayanin, ya nuna bai kamata a sayar da man a 108 ba abin da yafi kar ya wuce naira 70 a halin da kasuwar man fetur take a duniya.

PDP ta koka yadda gwamnatin tarayya da jam’iyar APC ke jagoranta ke tafiyar da abubuwan rashin tabbas ga mutanen kasa, ta kasa magance rashawa a haujin Man fetur an ki bari kasuwa ta yi wa kanta matsaya a sha’anin man fetur.

PDP ta nemi gwamnatin Buhari ta gaggauta rage kudin man fetur din, kuma ta yi amfani da biliyoyin da ta samu tun sanda aka samu canjin na faduwar man ta kawowa mutanen kasa sassaucin rayuwar yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *