Gwamna  Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi rashin mahaifinsa wanda shafe shekarru 96 a duniya, Shaikh Haruna Waziri Usman yaya ne ga mahaifin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

 Muhammad Bello mashawarci ga gwamn ya fitar da sanarwar rasuwar wadda aka rabawa manema labarai a jihar Sakkwato ya ce Allah shi ne mallakin komai  da haka yake sanar da rasuwar mahaifinsa Shaikh Haruna Waziri Usman.

Ya ce Margayin ya rasu a gidansa dake garin Tambuwal a yau Alhamis da shekarru 96.

 Shehi shi ne jagoran darikar Tijjaniya a garin Tambuwal gaba daya, ya yi wa addininsa hidima sosai al’ummar  garin Tambuwal da jihar Sakkwato musamman mabiya darikar Tijjaniya sun yi rashin gwarzo mai son taimakawa addinin musulunci.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *