Spread the love

Hikumar bayar da ƙididdiga ta ƙasa(NBS) ta fitar da rahoto a dukkan mutum 10 na ‘yan Nijeriya huɗunsu na cikin talauci.

Hukumar ta fitar da bayanin ne a Litinin da ya nuna mutanen Nijeriya miliyan 82.9 ke rayuwa cikin talauci.

Abin da masana suka aminta da shi wanda yake rayuwa kasa da dalar Amerika 1.90 bai iya samunsu balle ya kashe shi ne matalauci. Rahoton ya nuna duk mutum huɗu cikin 10 na mutanen Nijeriya ba su samun kudin.

Rahoton ya nuna jihohi uku da suka fi kowa talauci sun haɗa da Sokoto nada kaso 87.73, sai Taraba mai kaso 87.72, sai jihar Jigawa mai kaso 87.02.

Sun kawo jihohi uku da suka fi karancin talauci kamar Lagos mai kaso 4.5, sai Delta mai kaso 6.0 ta ukunsu Osun mai kaso 8.5.

Hukumar ta ce za ta buga cikakken rahoton talaucin a wata rana ta daban.

Bankin duniya a Disimban 2019 ya gargaɗi mahukunta a Nijeriya kan yanda ‘yan kasar ke faɗawa cikin matsanancin talauci.

A jihar Sokoto akwai buƙatar Gwamnati ta tashi tsaye ga samar da aikin yi ga matasa da kawo hanyoyin da kamfanoni za su shigo a jihar da ware tallafi don taimakawa ‘yan kasuwa manya da matsakaita, don ganin ta ajiye wannan baƙin kofi da ta ciwo a fadin Nijeriya.

Har zuwa rubuta wannan rahoton Gwamnatin jihar ba ta ce komai kan rahoton ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *