Spread the love

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya nada sabon shehun Bama, tare da gindaya masa sharadin zai zauna tare da mutanensa, ba wai ya koma Maiduguri da zama ba.

Sabon Shehun Bama Umar ibn Shehu Kyari ibn Umar Elkanemi shi ne babban dan shehu da ya rasu a satin da ya gabata a garin Maiduguri.

Sakataren gwamnatin Borno Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya gabatar da takardar kama aiki a fadar Sarkin Bama da ranar yau Litinin, amadadin gwamnan jiha.

Ya ce mai girma gwamna ya umarce ka da ka zauna cikin mutanenka domin ka yi masu jagoranci ku fa’idantu da juna.

Sabon sarkin kafin a nada shi sabon mukamin dan kasuwa ne da ya fice a yankin kuma ga shi matashi da ake sa ran ya kawo sauyi a masarautar Bama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *