Spread the love

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a jawabin da ya yi wa al’ummar  jihar kan halin da ake ciki kan cutar Korona ya ce  ya sanya dokar hana yawo da dare  a jiharsa daga Litinin 4 ga watan Mayun nan har sai yanda hali ya yi daga 8pm zuwa 6am a kowace rana.

Ya ce an samu karuwar cutar a jihar in da mutane suka kai 66 wadan da suka rasa ransu 8 jihar na cikin jihohi dake kan gaba a Nijeriya a yanzu, kuma jihohi suna kara daukar matakai na yakar cutar  domin wanzar da dokar shugaban kasa ne muka sanya dokarmu ta hana yawo.

Ya ce dokar ba ta shafi ma’aikata masu aiki na musamman ba, da ma’aikatan gwamnati da suka kai matakin na 13 zuwa sama da dokar zama gida ba ta shafa ba, amma su sanya takunkumin fuska kafin su tafi wuraren aikinsu ko mu’amala da mutane wannan kari ne na matakin da gwamnati ta dauka.

Akan haka gwamna Tambuwal ya roki mutane su cigaba da daukar matakan yakar wannan cutar, su daure su yi hakuri an yi haka ne domin kariya gare su don haka su zama ‘yan kasa nagari, ya kuma roki gwamnatin tarayya ta hannun kwamitin shugaban kasa na yakar cutar da ya tallafawa jihar da kayan aiki domin shawo lamarin kar ya wuce in da ake yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *