Spread the love

Daga Murtala ST Sokoto      

Shugabar kungiyar mata musulmi ta kasa Malama Amina Musa Sakaba ta bayyana cewa haduwar mata da maza shi ne silar yawaitar fasadi a cikin al’umma.

Malama ta furta hakan a lokacin da take gabatar kasida a cibiyar yada addinin

musulunci dake Sakkwato(IET), wadda cibiyar  ta  shirya, a cikin watan ramadan

domin ‘yan uwa mata.

Malama Sakaba ta kara da cewar “haduwar mata da maza bai  halatta ba sai da

wasu sharudda da suka hada da karatu, salloli, taron karawa juna sani, suma sai in an gudanar da su bisa ka’idodin shari’a.

 Tace  haduwar da mafi yawan mata da maza ke yi yanzu mussamman a wajen tarukan bukukuwa, kasuwanni da wuraren shakatawa shari’a ta yi hani akansu, kuma mafi yawan wadannan haduwar kan haddasa fasadi tsakanin mata da maza da zinace-zinace da aikata kaba’irori, hadisin Manzo(S.A.W) ya ce  gara a sokama mutum karfe daga kai har kasa,da ya tabi wace ba muharramar sa ba.

Amirar ta kara da cewa haduwar yakan haifar da abubuwa da dama da suka hada da,haifar da rashin kunya,samar da alaka mai mumunan karshe da  kuma samun wani karni na jama’a da basu san kawaici da kamun kai ba, da yawaitar sakin  aure, haifar da rashin yarda tsakanin ma’urata da kuma yaduwar curuta sakamakon alakar banza.

 Malamar ta yi kira ga iyaye da su saka ido ga yaransu, su kuma tarbiyartar da su akan nisantar duk wani wuri naalfasha, ta  yi kira ga matasa samari da ‘yan mata da suji tsoron  Allah su yi riko da tarbiyar da aka dora su akanta, su kuma guji duk

wani abu da Allah ya hana.

Ta yi kira  ga shugabanni da malaman addini da su kara kaimi wajen hana haduwar da ba ta da amfani da kuma sanya ido kan wuraren da ake hakan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *